Spread the love

Shirin wasan kwaikwayo mai dogon zango LABARINA da ake haskawa a gidan talabijin na arewa 24 dake saman tauraron dan adam bayan kammala zango na daya dana biyu ana sa ran daina cigaba da haska shirin a tashar arewa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan hasashen ya fara ne a lokacin da daraktan shirin Malam Aminu Saira ya fitar da bayani kan tukararsa game da cigaba da haska shirin.

Saira ya ce “Ina mai Alhinin Sanar da masoya wannan Shiri na #LABARINA Series cewa bayan gama Zango na 1 da na 2. antafi Hutu zuwa wani lokaci.
“In sha Allah ba da jimawa ba za mu sanar da lokacin da za’a dawo , da kuma tashar da zai cigaba da zuwar muku. “Muna masu baku hakuri muna godiya da soyayyar ku gare mu Allah yabar zumunci.” a cewar Saira.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shirin yana da dimbin masoya masu bibiyarsa hakan ya sa hankalin jama’a ya karkato da ba a nuna shirin ba don sanin dalilin samun tsaiko.
Al’adar masana’antar kenan da wuya shiri ya daukaka bai haifar da matsala a tsanin masu shiryawa da daukar nauyi da ‘yan wasan shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *