Spread the love

Zulum ya daura harsashin gina jami’a mai zaman kanta a Borno
A fili mai hekta 100,
Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a yau Litinin ya daura harsashin ginin jami’ar Al-Ansar, mai zaman kanta ta farko a jihar.
Watanni baya da suka wuce Zulum ya amince da bayar da hekta 100 a Maiduguri, ga gidauniyar Al-Ansar, wacce ke daukar nauyin aikin Jami’ar, a wani wuri da ke kan hanyar Gubio a babban birnin jihar ta Borno.
Shugaban gidauniyar ta Al-Ansar, Dakta Muhammad Kyari Dikwa, tsohon sakatare na din-din-din na tarayya ne ya kaddamar da aikin.
Zulum a jawabinsa wurin daura harsashin, ya ba da umarnin gina titin kilomita 2.3 a cikin jami’ar, baya ga ci gaba da aikin gina karamar rijiyar bohol da Gwamnatin ke yi a cikin jami’ar.
Gwamnan ya kuma umarci ma’aikatar Ilimi mai zurfi, Kimiyya da Fasaha ta bayar da kaya da yadda Gwamnatin Borno za ta kara tallafawa aikin.
Zulum ya yi alkawarin bayar da irin wannan tallafi ga duk mai son sanya hannun taimako ga Borno, musamman kan ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *