Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ziyarci Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a karon farko tun sanda Wamakko ya shiga gidan kusan shekara 16 kenan.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bafarawa ya tafi gidan domin yi wa Sanata Wamakko wanda shi ma tsohon gwamnan Sakkwato ne ta’aziyar rasuwar dan uwansa Dakta Bello Magatakarda Wamakko da ya rasu a jiya Assabar bayan gajeruwar rashin lafiya a garin Zariya jihar Kaduna .
Bafarawa tare da tawagarsa sun yi gaisuwa ga dangin margayin da abokansa da Sanatan.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

An gabatar da addu’a ta musamman wadda limamen masallacin Usman bin Affan Shaikh Yahuza Shehu Tambuwal ya gabatar.
Managarciya na tuna cewa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya dawo gidansa dake unguwar gawon nama a birnin jiha cikin shekarar 2006, bayan da alaka ta yi tsami tsakaninsa da mai gidansa Bafarawa wadda ta kai da har ya ajiye aikinsa a matsayin mataimakin gwamna jihar Sakkwato.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Tun a lokacin Bafarawa bai taka kafarsa zuwa gidan ba domin taya murna ko jaje, sai a wannan karo da suka sulhunta tsakaninsu.
Kusan wannan shi ne na farko da aka ga fuskar Bafarawa a gidan wanda hakan cigaban siyasa ne da jiha baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *