Spread the love

A shekarar da ta gabata ne 8 ga watan Oktoba Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya karyata labarin da ake yawo da shi kan cewa ya ayyana zai yi takarar shugaban kasa a 2023.
Jigo a jam’iyar bai ce ba zai yi takarar shugaban kasa a 2023 ba, a wani bayani da mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya fitar ya ce gwamnan ya mayar da hankalinsa ne kan samar da gwamnati mai kyau domin cin moriyar dimukuradiyya ga mutanen jihar Sakkwato.
Ka ga dai kenan maganar zai yi takarar shugaban kasa ba za a yi watsi da ita ba.
Matukar jam’iyar adawa ta PDP ba ta yanke hukuncin kai takarar shugaban kasa a kudu ba, waton aka turbude karba-karba, Tambuwal yana iya samun damar zama dan takarar shugaban kasa duba da yadda yake kan gaba daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyar.
Gwamna Tambuwal dai har yanzu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta yin takarar ba, amma dai a wani hannun a boye yana nan yana nema a karkashin kasa kuma da yawan jagororin suna goya masa baya, daga ciki har da gwamnoni dake saman mulki a yanzu.
Tambuwal Kalubalen da ke gabansa bai fi yanda zai gamsar da mutanen da suke ganin yakamata a baiwa mutanen Kudu damar tsayar da dan takara a jam’iyarsu ta PDP a wannan lokacin tun da dan Arewa ne zai kare wa’adinsa na shekara takwas, ba tare da la’akari da bambancin jam’iya ba. Ana yi masa kallon karawa da Atiku wata babbar barazana ce gare shi wadda dakyar zai sha, ko mine ne dai lokaci zai bayyana komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *