Spread the love

Bayan Kashe Manoma Bakwai Sakataren Gwamnati Ya Ziyarci Babban Rami

Daga M. A. Umar, Minna.

Bayan wani harin da aka kaiwa manoma a garin Babban Rami na karamar hukumar Mashegu da ya janyo mutuwar manoma bakwai, da jikkita wasu da maharan suka rutsa da su gona a lokacin girbin abinci a satin da ya gabata.
Gwamnatin Neja ta jajanta ma wadanda abin ya shafa a lokacin da sakataren gwamnatin jiha, Ahmed Ibrahim Matane ya ziyarci garin a madadin gwamnatin jihar dan jajanta ma al’ummar garin Babban Rami kan wannan rashin da maharan suka yanyo.
Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana cewar gwamna Abubakar Sani Bello ya himmantu wajen kawo karshen garkuwa da mutane da hare-haren maharan ga al’ummar jihar. Matane yace gwamnatin jiha na jajantawa iyalan mamatan ‘yan uwa da abokan arziki akan wannan rashin, inda ya bayyana cewar nan bada jimawa gwamnatin za ta kawo karshen wannan ta’addacin a jihar nan.
Ahmed Matane, yayi kira ga jama’ar jihar da su hada kai da gwamnati da jami’an tsaro wajen kawo karshen ta’addanci da hare-haren yan ta’adda a jihar nan, saboda wannan matsala ce da ya kamata a hada kai dan kawo karshen shi, dan ya shafi kowa.
Sakataren ya jawo hankalin al’ummar jihar wajen goyawa gwamnatin jiha baya a yunkurinta na fuskantar matsalar tsaro da ke mayar da hannun agogo baya wajen cigaban tattalin arzikin jihar da na al’ummarta, maganar tsaro abu ne da ya shafi kowa.
Matane ya jawo hankalin sarakunan gargajiya, malaman addini da shugabannin al’umma da su taimakawa gwamnati da bayanai kan ayyukan maharan da maboyarsu da ke yankunan su, wanda zai taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da yan ta’adda a jihar nan.
Da yake bayani, Alhaji Musa Adamu, Sarkin Babban Rami, wakilin hakimin Kaboji, ya yabawa gwamnatin jiha, bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sani Bello akan kulawa da kuma jajircewarsa wajen kawo karshen hare-haren maharan ga mutanen karkara da jihar baki daya.
Alhaji Adamu ya baiwa sakataren gwamnatin tabbacin cewar al’ummar Babban Rami, za su hada kai da gwamnatin har sai zaman lafiya ya dawo a garin Babban Rami da karamar hukumar Mashegu da jihar baki daya, ” za mu cigaba da yin addu’o’i da sanya idanu akan duk bakon lamari a yankin nan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *