Spread the love

Barayi sun kama ɗaya daga cikin mahautan dake siyen shanunsu.

Hauwa’u Salisu

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani mahauci mai suna BBC mazaunin Marina ya shiga dajin Batsari gun Ɓarayi ya siyo shanuwa guda ya ba da kuɗi rabi bai ida cika rabin kuɗin ba ya ɗauki lamunin wasu kwanaki zai kai masu cikon Kuɗinsu.

Sai dai kuma kafin zuwan ranar sai dai kawai ya gansu a gidanshi su ka buggugeshi suka tafi dajin da shi suka ce sai an kai masu cikon Kuɗinsu Naira dubu talatin da biyar za su sako shi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bayan da iyaye da danginshi suka haɗa kuɗin suka kai mashi sai suka ce ai sai an ƙara masu wasu kuɗin kan waɗan can domin kuwa an gaya masu yace ba zai biya kudin ba.

Daga ƙarshe dai sai da aka sake kai masu dubu talatin sannan suka sako shi yanzu haka hannuwanshi duk jini ya kume saboda daurin da sukai ma shi bai iya ɗaukar komi da su sai magani ake ma shi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Akwai bukatar jami’an tsaro su yi wani abu a jihar Katsina domin ɓata gari na yanda suke so a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *