Ashe Ɓarayi na yin biki su ma?

Hauwa’u Salisu

Wani kamemmen mutum mazaunin Sabon garin safana dake ƙaramar hukumar Dutsanma ya sha da ƙyar bayan tafiyar yan kidnapping ɗin da suka kamasu su biyu suka killace suna jiran kuɗi Naira miliyan biyu da rabi.

Mutumin wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya ce, ni tsautsayi ne yasa suka kamani domin ba guna suka zo ba gun makwabcina suka zo, sai ƙaddara tasa na fito don ganin abin da ke faruwa suka ganni.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sai kuwa suka buƙaci makwabcin nawa ya koma gidansa ni kuma na bisu don gano abin da ke faruwa sosai.

Ya cigaba da cewa babu irin wahalar da bamu sha a hannunsu ba domin babu ko abincin kirki hakama ruwa, sannan duk sun ɗaure mana idanuwa da baƙin ƙyalle ni da wani mai kiba da ban san kowaye ba

Muna tafiya suna dukanmu da bulala wai bamu sauri.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kwanakina shida wurinsu cikin daji suna ta waya gidana a kawo masu Naira miliyan biyu da rabi anata neman su sauƙaƙa domin dai babu kuɗin gaskiyar magana.

Kawai sai ranar asabar ɗin nan suka ɗumguma suka tafi bikin wani ɓarawon suka barmu mu kaɗai a ɗaure.

Cikin ikon Allah sai na kwance kaina domin daurin bai dauru sosai ba yana sauri wanda ya ɗaureni ya tafi gun bikin.

Ko da na kwance na sai na kwance wanda suka kamo mu tare na ce ma shi mu yanki daji muita gudu amma sai ya ce min shi kam ba zai iya gudu ba domin yana da kiba sosai.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ko da na ga da gaske bai guduwa sai na yanki daji nai ta gudu sai gani na ɓullo ta mararrabar safana anan ‘yan sanda suka ganni suka taimakeni domin kafafuwana duk sun fashe saboda azabar gudu su ne suka ida kai ni gida suka ban kyautar kuɗi .

Allah Ya rabamu da mugun ji da mugun gani .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *