Spread the love

A yau shekara daya da wata shida da aka zabi shugaban majalisar dokikin jihar Sakkwato Honarabul Aminu Muhammad Achida a matsayin wanda zai jagoranci majalisar dokokin dan jam’iyar adawa ne a jiha waton APC.
A lokacin da aka yi zaben jam’iyar ke da rinjaye da dan majalisa daya in da APC ke da mamnobi 16, PDP mai mulki a jihar Sakkwato nada 14.
Bayan watannin yana na jan ragamar Allah ya yi wa daya daga cikin ‘yan majalisar dokoki a jam’iyar APC Alhaji Isa Harisu rasuwa wanda yake wakiltar karamar hukumar Kebbe.


Hukumar zabe ta gudanar da zabe jam’iyar PDP ta samu nasara abin da ya mayar da mambobin majalisar daidai kowace jam’iya nada 15 jimlarsu 30 kenan.
Bayan hakan ne aka yi tsammanin shugabancin majalisa zai sauya, domin shugaban majalisa da ya kori kansa a jam’iyar APC lokaci ya yi da zai yi wa kansa matsaya ko ya shiga jam’iyar PDP da yake dasawa da jagororinta ko kuma ya nemi wata jam’iya ta daban daga cikin jam’iyyun da ake da su a kasar Nijeriya ya shiga, amma ba abin da ya faru daga cikin hasashen, kwatsam sai aka ji wani rummace a jagorancin majalisa in da aka yi jagoran APC Isa Ambarura da jagoran PDP Malami Muhammad Basakkwace, wannan sabon abu ne a tafiyar da majalisar dokokin jihar ta Sakkwato.

Managarciya ta tattauna da daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jiha na jam’iyar PDP Honarabul Aminu Almustafa Gobir wanda akafi sani da Boza mai wakiltar karamar hukumar Sabon Birni ta Arewa don jin tabakinsa ya yake ganin ko Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ya yi wa magoya bayan jam’iyar PDP adalci ya bar shugaban majalisar dokoki na yanzu ya ci gaba da jagoranci duk da yana da damar da yake sauya tafiyar ganin wasu a nesa na iya kallon kamar nakasu ne a ce jam’iyar adawa ke jan ragamar majalisar dokoki a gwamnatin PDP ya ce wannan ba daga bangaren Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ba ne, masu zabe ne, su da ke zabe kuma su ne suka zabi mutanen kowace jam’iya 15 a kowane bangare hakan ke nuna kowace jam’iya tana da karfi a Sakkwato.

Boza ya ce ya danganta mai girma gwamna shi ne zai samo alkibla wadda za ta iya samar da nasara ko akasinta.
“In mai girma gwamna ya kwatanta adalci za ka ga an wayi gari ya kwashe ‘yan majalisar da ba su gefensa, in bai yi ba za ka ga an kwashe mu.” a cewar Honarabul Aminu Boza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *