Spread the love

A ranar Assabar data gabata Suwaiba Naziru ýar shekara 22 dake dauke da ciki an ka yi garkuwa da ita a kauyen Biya ki kwana a karamar hukumar Batsari a jihar Katsina tare karamar ýarta mai shekara biyu.
‘Yan bindigan sun yi kauyen zobe da misalin karfe 8 na dare sun yi wa wasu mutunm biyu rauni ta hanyar harbi suka tafi da mata da yara su 10.
Bayan share dukan daren suna tafiya a cikin daji Suwaiba ta haihu a gaban ýan bindiga.
‘Yan uwar wadda aka yi garkuwa da ita sun sanarwa jaridar daily trust cewa mutanen suka kira suka labarta masu halin da ake ciki, kuma su samu babur mai karfi cike da fetur a tanki don su je su dauko mai jegon a Sabon garin Damburawa.
Sun ce ba su gamsu da maganar ba domin zargi duk wanda ya tafi suna iya rike shi tare da babur din da ya tafi a matsayin fansa. Da suka sake kira sai aka fada masu ba a samu babur ba har yanzu.
Sun ce daga nan ýan bindigar suka yanke shawarar kai mai jegon kauyen Dangeza daga nan ne aka aza ta saman babur aka kawota gida.
Suwaibar ta ce ta yi doguwar tafiya a daji da ba zata iya ganewa ba kafin nakuda ta taso mata.
“Duba ka gani ina da ciki gashi na goya ‘ya ta mai shekara uku, ka auna yanda zan sha wahala ko da ni kadai nike bana da juna biyu ban dauki ‘ya ta a baya ba duka a lokaci daya. Gaba daya mun shafe daren muna tafiya.” a cewarta.
Ta ce bayan ta haihu daya daga cikin matan da sato su tare ta yi mata unguwarzoma daya daga cikin mutanen ya ba ta reza ta yanke cibi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *