Hauwa’u Salisu (Haupha).

Wata mata dubunta ta cika a jahar Katsina cikin garin Safana inda ta shirya tsab ita da yaranta guda biyu da niyyar zuwa Katsina.
Sai dai bayan tafiyarta ne ta kira mijinta ta bayyana ma shi barayi sun sace ta sai ya tura masu kuɗi Naira dubu ɗari shida.

Matar an sakaya sunanta ta bayyana cewa, auren ƙanwarta ne za a yi su kuma basu da halin kuɗin kayan ɗaki, don haka suka shirya hakan.

Sai dai asirinsu ya tonu ne saboda sun amshi kuɗin ta hanyar account na banki.

Matar ta ƙara da cewa sai da suka shiga suka fita gun wani malami sannan sukai wannan damfara ta waɗannan kuɗaɗe.

Ta ƙara da cewa wani babban DSS ne ya binciko gaskiyar maganar inda ya bi diddiƙin bankin da aka tura kuɗin.

To Allah Ya kyauta ya rabamu da son zuciya.
Managarciya ta so jin ta bakin mijin domin sanin matakin da zai ɗauka a gaba, amma duk yuƙurin da aka yi ci tura.
Wata majiƴar ta ce mijin ya cigaba da zama da matarsa don ya ɗauki abin da ta yi kuskure ne a rayuwa.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *