Spread the love

Tambuwal ya nada shugaban ma’aikatan jihar Sakkwato

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya nada shugaban ma’aikatan jihar Mallam Abubakar Muhammad (Mni) wanda aka fi sani da dan shehu.
Hakan ya biyo bayan ritayar da tsoon shugaban Alhaji Sani Garba Shuni, ya yi don ya cika shekara 60 da soma aiki a Disamba 30, 2020.

Kafin haka ya yi aiki a kamfanin jarida na jiha a 1992 ta haka ya zama babban sakatare a 2008 a ma’aikatar gona ta jiha, ya yi zama a ma’aikatar yada labarai, da ilmi mai zurfi da lafiya kafin wannan mukamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *