Spread the love

Gwamna Abubakar Sani Bello Ya Tabbatarwa Al’ummar Jihar Zai Samar Da Gwamnati Mai Inganci

Daga M. A Umar, Minna

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya nemi al’ummar jihar da su cigaba da baiwa gwamnatinsa goyon baya dan ayyukan da za su kawo cigaba a jihar.
Gwamnan yayi wannan kiran ne a sakon sa ga al’ummar jihar na sabuwar shekarar 2021, inda ya bayyana cewar shekarar 2020 mai karewa ta kalubale da dama masu tsauri, inda ya bukaci al’ummar jihar da su zama masu kyautata tsammani da juriya, ta hanyar yin addu’o’i dan samun canji da kawo karshen matsalolin a shekarar 2021.
Gwamnan ya yabawa al’ummar jihar kan goyon baya da hadin kan da suke baiwa gwamnatin sa akan yaki da matsalar tsaro, da annobar COVID-19 da ya mayar da tattalin arzikin jihar baya, wanda ya shafi jihar da kasa baki daya.
Gwamnan yace gwamnatin sa na daukar matakan da suka dace kan dakile yaduwar annobar COVID-19 a jihar, ya nemi jama’a da su kara kaimi wajen bin dokokin da hukumomin lafiya suka tsara na kaucewa yaduwar annobar karo na biyu wadda tafi muni akan na farkon kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Dan gane da matsalar tsaro kuwa, yace gwamnatin jihar da ta tarayya suna aiki kafada da kafada dan samar da hanyoyin da za su kawo karshen sa a kasar nan, ya nuna takaicinsa kan yadda mahara suka samu damar baje kolinsu wajen kai hare-hare da garkuwa da jama’a wanda ya jefa rayukan jama’a cikin fargaba a kasar nan.
Gwamnan yace gwamnatin sa ta taka rawar gani wajen rage radadin talauci a jihar ta hanyar bunkasa bangaren noma da kyautata rayuwar jama’a, yace zai cigaba da taba wasu bangaroran dan samun rayuwa mai inganci a jihar.
Ya bada tabbacin cigaba da gyaran hanyoyi mallakin gwamnatin jiha, musamman hanyar Minna zuwa Bida, da kuma karin wasu hanyoyin da ke cikin birane da tabbatar da an kai wutan lantarki a yankunan karkara kafin kammala wa’adin mulkin nan.
Ya yabawa al’ummar jihar tare da jawo hankalinsu akan wasu batutuwa da suka shafi gwamnati ba tare da siyasantar da batutuwan da ba su tabbaci akan sa, gwamnati a kowani lokaci a shirye ta ke wajen karban kalubale da korafe kirafen jama’a.
Gwamnan ya baiwa al’ummar tabbacin cewar gwamnatin sa a shirye ta ke wajen samar da ayyukan da za su kawo cigaban jihar.
Gwamnan ya yabawa al’ummar jihar kan hadin kai da zaman lafiya, da juriya akan kalubalen da jihar ke fuskanta, wanda ya jawo hankalin su kan karin goyon baya dan cigaban jihar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *