Hauwa’u Salisu (Haupha).

A ƙauyen Sararraki dake cikin ƙaramar hukumar Safana, ‘ƴan bindiga daɗi sun yi gaba da da wani tsoho mai suna Malam Sale wanda ke zaune cikin ƙauyen Sararraki dake Safana.
Matar Malam Sale ta shaida mana cewa Suna zaune a cikin gidansu sai suka ji tsayuwar babur da yawa a ƙofar gidansu, kafin su yi wani motsi masu garkuwa da mutane sun kewaye su.

Ta ƙara da cewa, Malam ya gaya masu bamu da komi sai gero bai yi tiya guda ba.
Amma haka suka tasa mata miji suka tafi sai bayan kwana biyu suka kawo wata takarda suka saki a cikin gidan, sai matar ta ɗauka ta je cikin Garin Tambari da suke makwabtaka aka karanta mata.

A cikin takardar masu garkuwar sun nemi fansar Aa kai masu Sigari ta ɗari biyu sai batiran fitila na ɗari biyu.

Tsohuwar ta ce, Sai na dawo gida da nufin ɗaukar geron in saida in Sai masu abin da suka ce .

Washe gari sai ga wata takardar na kaita aka karanta min sun ce na sa yi batiran ko su kashe Malam su haɗa da ni.

Don haka na saida geron na sai batiran na aje masu inda suke yada takardar sai ga Malam sun maido.
Harkar fansa a jihar Katsina na ɗaukar sabon salo tana son ta koma sana’a a tsakanin manyan ‘yan ta’adda da kanana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *