Spread the love

Wamakko ya yi ta’aziyar rasuwar Iyan Zazzau

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana rasuwar Iyan Zazzau na Zariya a jihar Kaduna babban rashi ne ba ga jihar kadai ba ga Nijeriya baki daya.
A sakon ta’aziya Wamakko ya ce margayin Bashar Aminu ya bayar da gudunmuwa ga cigaban kasa tsawon lokaci da yake raye.
Wanakko musamman ya jijinawa margayi a kokarinsa na hada kan kasa da tafiya tare.
Wamakko ya nuna lalle tarihi ba zai taba mantawa da iyan Zazzau ba kan gina kasa da gudunmuwarsa ga masarautun gargajiya.
Margayin ya rasu yana shekara 70 a duniya ya bar babban giɓin da ke da wahalar cikewa.
A yau Jumu’a ne ya rasu Sanatan a wani bayani da mataimaka masa kan harkokin yada labarai Bashir Rabe Mani ya fitar ya roki Allah ya gafartawa mamacin.
Ya yi gaisuwa ga iyalai da gwamnatin Kaduna da mutanen kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *