Spread the love

Tukunyar  turawa ba su yi wa kasuwarmu barazana sai dai—Shugaban masu tukanen karfe 
 
Kasuwancin masu samar da tukanen karfe da wasu ke kira tukunyar alminiyum da ake girki da su daden zamani a kasar Hausa, wasu na ganin samar da tukunyar zamani da turawa suka yi da ake sayarwa a manyan shaguna  a kasar nan zai  iya taba kasuwancin ko ya kawar da shi gaba daya. 
Manema labarai sun ziyarci masana’antar da ake kera tukanen waton Makera a unguwar kara dake jihar Sakkwato don ganin yanda kasuwancin ke tafiya.
Suleman Gulma dan shekara 48 da haihuwa shi ne shugaban masu wannan sana’ar a jihar Sakkwato ya ce ya shekara 33 cikin sana’ar akalla suna da mambobi 450 dake cin abinci a masana’antar.
“Kalubalen da muke fuskanta na kayan aiki da muke amfani da su ne domin kamfani ke sayen kayan kuma mu ba mu iya saye yadda kamfani ke saya kusan shi ne abin da ke damunmu ba wadataccen jari.
“Kan shigo da kayan zamani na girki har yanzu yawan masayanmu ba su canja ba domin mutanen karkara kayanmu suke saya da yawan mutanen birni ma haka, saboda turawa ba su da Tukunya Lamba 10 da 15 da 20 da 30 da  40, da zaran abinci yakai na mutum shida sai namu na turawa ba ya daukar abinci mai  yawan, kuma namu sun fi inganci nasu sun fi tsada, sauyin zamani bai taba kasuwancinmu ba muna da sauran cin abinci a kasuwar.” a cewarsa. 
Ya ci gaba da cewa a kullum masana’antar tana samar da akalla tukunya 1000, ya godewa gwamnatin Wamakko da ta ba su filin kasuwar ya nemi gwamnatin Tambuwal ta zagaye masu kasuwar don samar da tsaro da tsarin rufewa da budewa. 
“Ba mu taba samun tallafin gwamnati ba Allah bai kaddara ba duk da kasuwancinmu yana habaka a baya yini daya ba zai wuce ka yi Tukunya 25 ba kuma sai a cikin dare, a yanzu kuwa mutum daya sai ya yi Tukunya sama da 50 cikin kankanen lokaci domin mun samu yanayi mai kyau da kayan aiki.
“Farashin Tukunyarmu da muke kasawa a kasuwa lamba 10, 3500 sai 9, 3000, 8, 2500, 6, 2000, 5, 1700, 4, 1800, 3,1500, 2, 1200, sai lamba daya ta karshe 800.
Kayan sun yi tsada saboda yanda muke samun alminiyum da hodar da muke sawa tukunya ta yi fari sosai, farar kasar muna samunta ne a garin Kalmalu cikin karamar hukumar Illela a jihar Sakkwato.  Muna da bukatar tallafi don inganta sana’armu al’umma su samu a matasa masu aiki wani a yini zai samu 5000 wani kasa ga haka ya danganta.” acewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *