Spread the love

Gwamna Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya saukar da shugabannin kananan hukumomin jihar 23 saman mukamansu bayan kwashe shekara biyu suna rikon kwarya ba a gudanar da zabe ba.

Gwamnan a wani zaman da ya yi da Kantomomin Kananan Hukumomin a fadar gwamnatin jiha a yau Jumu’a ya ba da umurnin sauke su daga mukamansu a nan take abin da ake ganin ya zo masu da ba zata.
Tambuwal ya godewa tsoffin shugabannin kan aikin da suka yi ya kuma alkawanta masu duk wanda bai yi nasara takara neman sake dawowa shugaba ba, za a yi da shi in haka ta taso. In ba a samu dama ba ana nufin su yi hakuri.

“Dukkanku kun sani doka ta tanadi duk wanda zai yi rikon kwarya kar ya wuce wata shidda amma ku kun share shekara biyu.

“Nasan wasu daga cikinku na son su yi takara, ina yi maku fatan alheri. Duk a cikinku ko mutum ya yi nasara a zabensa ko bai yi ba, za mu sa shi aiki in dama ta samu.” a cewar Tambuwal.

Ya ce hukumar zabe ta jiha za ta sanar da tsare-tsarenta a lokacin da ya kamata.

Dayawan mutane sun yi farincikin wannan mataki da aka dauka a karamar hukumar Sakkwato ta Kudu domin yanda aka kasa samu jagoranci mai cike da kulawa da fahimta a karamar hukunar abin ya damu mutanen wurin musamman yanda tsohon shugaban ya mayar da kayan gwamnati ganima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *