Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

“Ina taya dukkan ‘yan Nijeriya murnan wannan lokaci na murna da fatan alkhairi da cigaba a shekara ta 2021.
“Shekarar 2020 ta zo ma daukacin kasashen duniya cike da kalubale na tattalin arziki, tsaro, lafiya da sauran fannunuka. Alhamdulillah duk da haka, wadannan kalubalen basu karya mana gwiwa na ganin samun kyakykyawar makoma a matsayin mu na mutane da kuma kasa.”
Wannan bayanin na kunshe ne a sakon taya murna ga yan Najeriya, da shugaban majalisar dattijai, Dakta Ahmed Lawan ya fitar.
Ya cigaba da cewar a matsayin mu na majalisar dokoki, mun dade da tsara yadda zamu tunkari abubuwan da shekarar 2020 ta zo da su ta hanyar yin dokokin da zasu tabbatar da gudanar da kyakykyawan mulki da cigaban tattalin arziki. Tun kafin zuwan shekarar mun sake fasalin tsarin kashe kudi na shekara-shekara ya koma daga watan Janairu zuwa Disamba kuma muka tabbatar kasafin kudin mu na 2020 ya tafi a kan wannan sabon tsarin. Mun yi wannan canjin ne don inganta harkokin tattalin arziki da bunkasarsa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Barkewar annobar Korona da ta yi sanadiyar rufe tattalin arziki ta yi mummunar illa ga dukkan kasashen duniya kamar yadda ta yi ma hasashe da tsarin tattalin arzikin mu. Daya daga cikin mummunan sakamakon haka ga Nijeriya shi ne kara fadawa cikin matsin tattalin arziki yan shekaru bayan fitar mu daga na baya.Duk da wannan yanayin, muna iya godiya ga Allah ganin cewa masifar harkar lafiya da ta matsin tattalin arziki da ta shafi duniya ba ta yi irin tasirin da kwararru su kayi hasashen za suyi akan Nijeriya ba.
Ya ce Ya yi imani cewa wannan ba wai sa’a gare su ba, amma sai don rashin jinkirin mu na daidaita da sake tsare-tsaren mu su dace da sabon yanayin da muka tsinci kanmu a ciki.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sake bullar annobar ba zai yi mana irin illar da wasu kasashe ke fuskanta ba, matukar gwamnati da mutane ba su yi sakwa-sakwa ba kuma muka dauki darasi daga abubuwan da ke faruwa a wasu wurare.
Don haka muna bukatar shiryawa fiye da lokacin baya don tunkarar 2021 da shekaru wasu zuwa gaba. Dole my tabbatar da mulki na gari ga mutanen mu da samar masu romon dimokaradiyya duk da kalubalen da muke fuskanta.
Majalisar dokoki ta 9 ta tsaya tsaye akan akidar ta na tabbatar da amincewa da kasafin kudi a watan Disamba kafin shigowar shekarar da za’a kashe kudaden, kuma mun yi haka ma a shekarar 2021. Hakanan, mum amince da kudurin dokoki masu yawa da bangaren zartaswa suka gabatar a matsayin dokar kudi don bada goyon bayan mu ga aiwatar da kasafin kudi na 2021 a cikin tsanaki. Mun sha alwashin ganin Nijeriya ta fita daga matsin tattalin arziki a cikin gaggawa a sabuwar shekara.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Don cin ma wannan burin namu, mun amince da bukatar bangaren zartaswa na samun izinin ci gaba da amfani da kudaden da ba ayi amfani da su ba na ayyukan raya kasa na 2020 har zuwa watan Maris na 2021. Mun yi ammana cewa barin a aiwatar da wannan bangare na ayyukan raya kasa na kasafin kudin 2020 kafada da kafada da kasafin kudi na 2021 zai samar da karin kudade ga tattalin arziki.
Karin muhimmanci, wasu daga cikin dokoki masu tasiri da ba mu iya aiki akan su ba a 2020 sakamakon abubuwan da suka faru da na ambata, a yanzu suna kan gaba a jadawalin mu na 2021.
Na farko a kan gaba shi ne kudurin dokar sake fasalin bangaren hako man fetur, watau Petroleum Industry Bill (PIB), da muke bukata don habaka bangaren mu na mai da iskar gas. Kudurin dokar PIB ta gagara wucewa tsawon shekaru amma munci dammarar ganin mun karya wannan lagon mun amince da kudurin a karshe kwatar farko ta shekarar 2021. Yana daga cikin burin mu, muga cewa kafa dokar PIB ya zama daya daga cikin abin tunawa da majalisar dokoki ta 9.
Hakanan, kudurin gyara ga dokar zabe yana kan gaba a jadawalin mu. Wannan ya zama wajibi don inganta tsarin zabe ya zama mai inganci da sahihancia kasar mu.
Mun sha alwashin amincewa da kudurin na gyaran dokar zabe kafin zango na biyu a shekarar 2021.
Ya ce har ila yau a kan gaba a jadawalin mu shi ne gyaran kundin tsarin mulki na 1999, wanda shi ne babban abinda ya hada mu a matsayin kasa daya. Yana cikin jadawalin mu, mu tabbatar mun gama aiki akan gyare-gyaren a cikin shekarar 2021. Wannan aikin da aka fara a 2020 yana bukatar tattaunawa mai zurfi da samun goyon bayan kowa da kowa.
Zamu bada goyon bayan mu cikin gaggawa ga kowane mataki don shawo kan annobar Korona.
A wannan bangaren, majalisar dokoki ta kasa tana jiran bangaren zartaswa ya gabatar mata da bukatar karamin kasafin kudi domin sayen allurar rigakafin cutar korona. Amma kafin nan, ya wajaba mu cigaba da kula da matakan kare kai da hukumomi suka gindaya.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Matsalar tsaro a kasar nan ta kasance gaba a kowane lokaci a jadawalin mu a 2020. Muna fatan cigaba da aiki da bangaren zartaswa domin samun mafita ta dindindin da zata maida kasar mu mafi tsaro da kwanciyar hankali.
Fatan mu na yin wannan ayyukan da karin cin nasara ya dogara ne akan hadin kan majalisar dokoki ta tarayya ta 9, tun daga kaddamar da ita, majalisar ta ke aiki ta hanyar sa kishin kasa a gaba ba tare da la’akari da siyasa ba. Wannan matsayin ya kara samun tasiri ne daga zamantakewa ta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin majalisa da bangaren zartaswa da muke sa ran zai dore a sabuwar shekara da ma bayan ta. Ya zuwa yanzu kowa ya ga alfanun da aka samu ta wannan kyakykyawar dangantakar tsakanin bangarorin gwamnati biyu.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaban majalisar dattawan ya cigaba da cewar ina mika godiyata ga dukkan yan Nijeriya saboda fahimtar su da goyon bayan su ga majalisar dokoki ta tarayya ta 9. Mun yi alkawarin cigaba da yin bakin kokarin mu akan tabbatar da mulki nagari da inganta rayuwar mutanen mu a sabuwar shekara.

A karshe shugaban majalisar dattawan yace ina kara mana fatan murnar sabuwar shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *