Spread the love

Kungiyar Manoma ta kasa reshen Neja ( AFAN) da hukumar wayar da kan manoma ( Simplelink Network Agency ) sun sha alwashin karfafa guiwar manoma musamman noman rani a masarautar Katcha.
Babban wakilin Simplelink a Neja, Amb. (Dk) Nura Hashim ne ya bayyana hakan ga wakilan mutanen Katcha da suka ziyarce a sakatariyar AFAN ta Neja.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dk. Nura ya cigaba da cewar akwai shirye shirye da dama da babban bankin tarayya ta kirkiro dan karfafa guiwar manoma musamman ganin yadda annobar Korona ta zamewa duniya damuwa da yasa tattalin arzikin ke yin baya, wanda idan aka karfafa guiwar manoman kasar za a kawo karshen shigo da abinci daga kasashen waje kuma yan kasa za su iya samun ayyukan yi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yanzu haka akwai shirin noman shinkafa na rani da yazo da sabon salo, ta yadda za a baiwa manoma irin shinkafa da aka fara horarwa wanda su dasawa kawai za su yi, sannan akwai shirin noman tumatur na rani da kuma shirin karfafa guiwar mata manoma, wanda za mu yi hadin guiwa da AFAN dan ganin al’ummar Katcha sun anfana.
Aikin da muka sanya a gaba yanzu shi ne yadda za mu karfafa guiwar kananan manoma da tallafin gwamnati dan samun karin gurabun ayyuka ga jama’a, kamar yadda na bayyana Simplelinks a shirye take wajen hada karfi da karfe da masarautar Katcha ta yadda al’umma.za su anfana.
Malam Umar Dan-asabe, shi ne sakataren tsare tsare na kungiyar AFAN, yace lallai AFAN a shirye ta ke wajen karfafa guiwar kananan manoma da duk wani tallafin da aka bayar dan su, kungiyar su za ta cigaba tsayawa wajen ganin manoman jihar sun iya wadatar da jihar da abinci.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kamar yadda na fada duk da cewar shiri yayi nisa wajen bada tallafin kayan aikin gona ga manoman jihar nan, hakan ba zai hana mu baiwa mutanen Katcha damar cin moriyar shirin ba.
A bayaninsa ga kungiyoyin, Kwamred Adamu Katcha, ( Ya- Ummah Teacher) yace Allah ya azurta kasar Katcha da filin noma mai yalwa musamman noman rani da na damuna, wanda yake baiwa baki damar shigowa daga wasu jahohin dan yin noma su samu arziki. A yanzu matasan mu da ke rige-rigen zuwa bariki dan neman kudi sun fara mai do da hankulansu gida dan yin noma, wanda wannan shirin na gwamnatin tarayya zai karfafa guiwar matasan Katcha wajen dogaro da kansu.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Gaskiya kamar yadda ku ka ba mu tabbaci a yau, in har kuka cika mana wannan alkawalin, ina ba ku tabbacin kasar Katcha za ta zama abin alfahari gare ku a bangaren noman rani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *