Spread the love

Babbar kotun jihar Jigawa ta bayar umarnin kashe mutum biyu ta hanyar ratayewa.
Mutum biyu da kotu ta ce a kashe su ne Mustafa Idris da Jamilu Harisu sun fito ne a daga kanan hukumomin Ringim da Farko.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A lokacin da yake yanke hukunci Alkali Ahmed Abubakar ya ce Idiris Mai shekara 29 da haihuwa ya fito daga kauyen Daneji karamar hukumar Ringim an same shi da laifin kashe budurwarsa Nafisa Hashim wadda suke Kauye guda. Za a kashe shi ta hanyar ratayewa.
Alkali Abubakar ya ce laifin da ya aikata ya sabawa kundin doka na 221 a tsarin dokar jiha.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shi ma Harisu za a rataye shi saboda ya kashe mahaifinsa Malam Harisu Bako a kauyen Maku cikin karamar hukumar Garki.
Shima laifinsa ya sabawa dokar jiha a Colin sashe na 221.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *