Spread the love

Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta aminta da nada uwayen kasa guda shida a jihar.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata takarda da aka baiwa manema labarai wadda kwamishinan ma’aikatar kula da kananan hukumomi da sarakunan gargajiya Honarabul Hassan Shalla ya sanyawa hannu.
Sabbin uwayen kasar da aka nada sun hada da Alhaji Sadik Ibrahim Uban kasar Birnin Kebbi(Ubandoman Gwandu) a karamar hukumar Birnin Kebbi da Aljaji Tukur Umar Bahindi uban kasa na Bahindin Bahindi a karamar hukumar Bagudo da Yakubu Abubakar Ka’oje uban kasar Yamusa(sarkin Yamusa).
Sauran su ne Buhari Muhammad Dangaladima uban kasar Alero a karamar hukumar Alero Alhaji Aliyu Mayama uban kasar Mayama(Sarkin kudun Mayama, sai Muhammad Nagwandu uban kasar rafin Zuru a karamar hukumar Zuru.
Kwamishina ya taya murna ga wadanda aka zaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *