Spread the love

ME YA SA MATAN YANZU BASA SON SAKA KWALLI A IDONSU?

Daga RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL SOKOTO.

Kwalli wani abu ne dake taka muhimmiyar rawa wurin ƙara fito da kyan kwalliyar Mace, sannan yana da matuƙar muhimmanci ko a lafiyar idanun, domin za ka ga hatta ƴaƴa maza jarirai ana saka masu kwalli domin ya ƙara musu ƙwarin ido.

A wannan zamanin mata da yawa basa son saka kwalli, saboda wasu dalilai na su.

Wasu rashin sabo da shafa kwallin ne tun yarinta, wasu kuma ciwon ido ke hana masu shafawa, wa su kuma sun ɗauki hakan matsayin ƙauyanci.

Wasu ma ba su ɗauke shi da muhimmanci ba kwata-kwata saɓanin Matan da da suka san muhimmancinsa sosai.

Bincike ya nuna cewa yanzu an ɓata kwalli saboda canza wasu sinadaran da ake amfani da su, da akwai wani kwallin Taya da ake yi yanzu, shi irin wannan kwallin shi ne zaka gan shi mai maiƙo sosai, sai ya kasance da Mace ta shafa sai ya dinga narkewa yana gangarowa ƙasan ido wanda hakan ke ɓata mata kwalliya.

Wani zubin ma idan ka shafa irin shi sai ka ji idonka na ƙaiƙayi da ruwa daga nan sai ciwon ido.

Wannan dalilin ya saka wasu mata suka daina shafa kwalli domin Mace ta tsani abinda zai ɓata mata kwalliya.

Baya ga wannan ma akwai wasu nau’ukan kwalli na Zamani da suke zuwa da siffar fensir kala-kala, akwai irinsu eye fensir, eye liner da sauransu.

‘Yan matan yanzu sun fi amfani da irin waɗannan a matsayin kwalli saɓanin ordinary kwalli da muka sani tun asali kaka da kakanni baƙin kwalli ko fari.

Mata a ci gaba da yin ado da kwalliya domin zama ƙasaitacciyar Mace isasshiya a ko da yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *