Spread the love

Shugaban karmar hukumar Shiroro a jihar Neja Kwamared Suleiman Dauda Chukuba an tsige shi daga saman kujerarsa.
An tsige Suleiman ta hanyar jefa kuri’ar amincewa da kasilolin karamar hukumar 11 daga cikin 14 suka yi a zaman da suka yi a Kuta hidikwatar karamar hukumar.
An saukar da shi ne kan zargin da ake yi masa na barnata kudin karamar hukuma da kuma fitar da kudin haraji na karamar hukuma wadan da suka yi batan dabo ba tare da amincewar majalisar karamar hukuma ba.
Kansilolin sun zarge shi cinye miliyan 7 da suka bayar da umarnin a fitar domin shirya taron karawa juna sani amma ba a yi taron ba tsawon wata hudu kenan.
Zaman tsigewar ya samu halartar dukkan kanilolin 14 wanda jagoran majalisa Malam Yusuf Aliyu ya jagoranta.
Dukkan kansilolin sun tafi gidan gwamnatin jiha domin tattaunawa da wasu muhimman mutane bayan sun gama zaman.
Rasuwar daya daga cikin kansilolin ne ya rage yawansu daga 15 suka koma 14.
Duk yunkurin da manema labarai suka na yin magana da tsohon ciyaman da aka tsige ya faskara, domin wayarsa ma a kashe take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *