Spread the love

Maganar da Bishop Mathew Hassan Kukah ya yi ta haifar da cece ku ce a tsakanin al’ummar Nijeriya, in da yake cewa kasar ta kasa a mulkin Buhari.
Fadan na Sokoto a jawabinsa ya daura laifin nuna fifiko da shugaba Buhari ke yi, ya ce da dan kudancin Nijeriya ne ke mulki da yanzu an kawar da gwamnatinsa matukar ya yi daya bisa ukun abin da Buhari ya yi a yanzu da yake saman mulki.
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kalamansa ta nuna suna haifar da kiyayya da rashin hadin kai a cikin kasa.
Kungiyar masu kula da harkokin musulunci(MURIC) a Nijeriya sun bayyana Kukah yana kira ne da a zo a yi juyin mulki daraktan Kungiyar Farfesa Ishaq Akintola ne ya sanar da hakan a wani bayani da ya fitar ya tir da kalaman Kukah da ya nuna musulunci addinin tashin hankali ne kuma ya bayyana shi a matsayin wanda yafi iya bata abu ba bisa gaskiya ba.
Kungiyar kiristoci a jihohin arewa 19 da Abuja sun goyi byan Kukah cewa ba a fahimce shi ba ne an juya kalaman domin kawo hatsaniya a kasa.
Mataimakin shugaba John Hayab ne ya fadi hakan ya ce ya nuna yanda gwamnati ta kasa ne kan tsare rayuwa da dukiyoyin ‘yan kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *