Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Gwamnatin Neja na neman tallafin gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kan su kan ma’adinan kasa, mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan ma’adanan kasa, Kwamred Abubakar Abdullahi Kuso ne ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da yake karba tambayoyin su a sakatariyar HYPADEC da ke minna.
Kuso ya cigaba da cewar Neja na daga cikin jahohi mafi karfin tattalin arziki a kasar nan amma kusan ba ta samun tallafin gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu yadda ya kamata. Ya kamata kamfanonin da ke hakar ma’adanai su rika cika alkawurran da suka dauka kafin gwamnatin tarayya ta ba su lasisi ta yadda jama’ar da ake hakar ma’adinan a yankunan su zasu anfana.
Yanzu muna da shiri na musamman akan tantance masu hakar ma’adinai na gaskiya da na bugi, wanda muna fatar idan shirin ya kan kama za mu iya tantance baragurbi da masu gaskiya musamman ganin irin halin da tsaro ke ciki a jihar nan. Wannan shirin zai ba mu damar samun cikakkiyar bayanai na masu hakar ma’adinai, yin haka zai taimakawa gwamnati da jami’an tsaro wajen yunkurin su na dakile yan ta’adda.
Ya cigaba da cewar ” yanzu haka muna da rahoton cewar kungiyoyi masu zaman kan su da ke bada tallafin suna jihar Fulato wanda muna bin hanyoyi ta hannun sakataren gwamnatin jiha ta yadda Neja ma za ta anfana da irin wannan tallafin.”
Mun zauna da kungiyar direbobin tifa masu hakar kasa da kungiyar masu hakar ma’adinai a karkashin kasa ta yadda idan sun kammala ayyukan su za a iya gyara muhallan dan kar su cigaba da zama hadari.
Kwamred Abubakar Kuso ya nemi al’ummar jihar Neja da su cigaba da baiwa gwamnatin jiha, bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sani Bello goyon baya domin tana da kudurce kudurcen da in an samu goyon bayan jama’a jihar za ta cigaba sosai.
Dangane da matsalar COVID-19 kuwa, yace gwamnatin jiha na bakin kokarin ta wajen ganin ta karya lagon hana yaduwar annobar a cikin al’umma, ta hanyar bin dokokin hukumar lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *