Spread the love

Rashin jituwa ta kunno kai tsakanin ma’aikata da masu karɓar fansho a jihar Kano kan zargin mayar da su saman tsohon albashi na dubu 18 tsohon tsarin mafi ƙarancin albashi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aminta da mafi ƙarancin albashin 30,600 a watan Disamba 2019, bayan wata shida da amincewar gwamnan yab riƙa zaftare kuɗin albashin ma’aikata daga kashi 10 har zuwa kashi 23, abin da ya fusata ƙungiyar ƙwadago ta jiha ta ba shi wa’adin sati biyu ya gyara lamarin.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bayan zama daban-daban gwamnati da ƙungiya suka cimma matsaya gwamnati za ta cigaba da biyan albashin kan ƙarancin biya 30,600, amma ba za ta biya ariyas daga watan Junairu zuwa Mayu ba.
Jaridar daily Nigeria ta samu bayanin cewa gwamna ya saɓa alƙawalin matsayar da aka cimma ya mayar da biyan tsohon ƙarancin albashi na dubu 18.
Gwamnan ya biya ma’aikayansa a watan Nuwamba da Disamba tsohon albashi ya kuma rage kuɗin fansho da kashi 15.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaban ƙungiyar ƙwadago na jiha Kabiru Ado ya ce gwamnati ba ta tuntuɓe su ba kafin ta mayar da biyan albashi da tsohon tsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *