Spread the love

Daga Rukayya Ibrahim Lawal.

JAN BAKI: Wani sinadari ne dake ƙarawa kwalliyar mata kyau da armashi, kuma akwai sirrin jan hankali a tattare da shi.
Duk kwalliyar da ba jan baki a cikinta ba ta kai kwalliya ba.
Saboda Muhimmanci jan baki, a wani shuɗaɗɗen zamani kafin zuwan Jan-baki dake zuwa cikin samfura kala-kala na Zamani, Mata sukan ci fure don bakinsu ya yi ja, haka kuma suna amfani da fure su goga a leɓensu don armashin kwalliyarsu.
Shafa jan baki yana ƙarawa kwalliya armashi ainun, saboda zan iya cewa ido da baki ne ke fito da kyawun kwalliyar da mace ta yi.
Shafa jan baki ya kan sa mace ta yi kyau, kuma kwalliyarta ta ƙara kyau da ita sosai.
Jan-baki yana ƙara fito da sirrin kyawun kwalliyar mace, yana saisaita baki sosai, sannan ana bin matching colours saboda Mace ta ƙara fitowa cas-cas abinta.
Zancen Gaskiya fa Jan-baki nada tarin muhimmanci da amfani ga kwalliyar mata, domin ita wata aba ce da ke son ado da kyatarwa.
Mace ta dauki jan-baki daya daga abubuwa masu muhimmanci a lokacin kwalliyarta da take son ta burge ta haska ta cinye a lokaci guda.
Abinciken da Managarciya ta yi jan baki na taimakawa mata wurin hana tsagewar labbansu na sama da kasa, domin fatar leben mata ya fi na maza zama dan siriri matukar baya samun danshi irin na sinadarin man jan baki zai tsage, abin da zai iya taba kyanta na zahiri.
Wasu mata ba su shafa jan-baki amma sukan samu man da ke dauke irin sinadarinsa domin kare fatar lebensu.
Jan baki na cikin abin da mata ba su wasa da shi, don gudun faduwar farashinsu, ko kazantar da kwalliyarsu.
Jan baki yakan saisaita kwaliyar mace ta fito gwanain shawa fiye da wadda ba ta sanya ba, goga shi iyawa ne da kwarewa a tsakanin mata za ka samu wata ta goga mai tsada amma don ba ta iya ba, wadda ta goga mai rahusa yafi nata fita da kyan kallo, Hoda ce kawai tafi jan baki muhimmacni a tsarin kwalliyar mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *