Spread the love

Usman Muhammad ya ce a zahirin gaskiya abin da ya shafi amfaninsu daban-daban ne, amma duk da haka lafiya ta fi kudi muhimmanci domin da ita ake isar da duk wani sako da lafiya ne za ka nemo kudin, ba shi ba ma mutum nawa ne ke da kudi ba su amfane shi ba kan rashin lafiya, in kan amfani ne ba su haduwa lafiya na gaba kudi nesa ba kusa ba, in kana da lafiya za ka iya nemo kudi amma in ba lafiya baka iya nemo komai.

Saliha Malami na ganin ai lafiya tafi kudi ba su haduwa amfaninta yafi na kudi don ko ga su in ba lafiya ba su da wani amfaninka, lafiya tana gaba da komai a rayuwa jin dadi da morewa sai da lafiya, mutum nawa ne za a kawo masa nama da madara ba zai iya sha ci da sha ba kan ba lafiya, amma duk ga mu nan don muna da lafiya ce ake magana da mu ga mai kudi ce an rufe a daki don ba lafiya. Ka duba da kyau ka gani lafiya na samo kudi amma kudi ba su iya sayen lafiya.
Da yawan mutane nada mabanbantan ra’ayi kan haka amma dai masu ganin lafiya ta rinjayi kudi sun fi yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *