2023:Rikicin jam’iyar PDP na ƙara ƙamari a jihohin Nijeriya

A ƙalla jihohi 12 ne suka tsunduma cikin rikicin wanda zai riƙe jam’iyar PDP kan kakar zaɓe mai zuwa ta 2023, manya a jihohin suna jayayyar jan ragmar PDP a jihohin.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Jihohin da ake ta wannan jayayyar sun ƙunshi Lagos,Ogun,Osun,Ekiti,Neja,Nasarawa, Filato, Adamawa, Kano,Cross river, Ebonyi, da Edo. Bayan Edo da cross river da Adamawa sauran jihohi PDP ce jam’iyar adawa.
Jihohin Lagos da Adamawa da Ekiti da Ebonyi da Osun da Filato sun dauki matakin shari’a tsakaninsu da shugabannin gudanarwar PDP na ƙasa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugabannin a kwanan baya sun kafa kwamitin sasantawa a tsakanin masu jayayyar wanda Sanata Bukola Sarki zai jahoranta, ɗaya daga cikin shugabannin ya ɗaura laifin haɓakar wutar ga shugabanninsu.
Ɗaya daga cikin jagorori a Adamawa Umar Arɗo ya ce su suna kotu ya ɗaura laifin rigimar ga shugabannin riƙon ƙwarya da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *