Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Rahotanni da ke fitowa shirye shiryen samar da sabon kundin tsarin jam’iyyar APC zai mayar da hankali wajen mutunta tsarin dimukuradiyya mai ingantaci, kamar yadda wani rahoto mai tushe ya bayyana.
Rahoton ya bayyana cewar jam’iyyar za ta yi nazari kan yadda ake baiwa tsoffin ‘ya’yan jam’iyyar takara ba tare da taƙaddama ba, ta yadda masu sha’awar shigowa za su samu damar yin takara ba tare da an tauye masu hakkin takara ba.

Binciken mujallar MANAGARCIYA ta jiyo cewar an nemi a canja tsarin wadanda ya kamata su zama mambobin kwamitin amintattun jam’iyyar.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Majiyar tace kwamitin dattawa, da ya shafi shugaban kasa mai ci da tsoho, mataimaka shugaban kasa, shugaban majalisar dattijai da mataimakinsa, da shugaban jam’iyya ta kasa na jam’iyya mai mulki wadanda ‘ya’yan jam’iyyar ne, zasu rika haduwa dan walwale matsalolin jam’iyya.
A cewar wani jigo a jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da wannan kudurin na sabunta tsarin da ake akai ga manema labarai.
Majiyar tace, ” Idan wannan kudurin da ake bukata ya tabbata za a samu canji mai anfani a jam’iyyar APC. Muna bukatar samar da majalisar dattawan jam’iyya wadda za a maye gurbinta da kwamitin amintattu, wadanda aka kasa rantsar da su tun bayan kafuwar jam’iyyar. Da su na aiki da ba mu samu matsalolin da muke fuskanta ba yanzu ba”.
Mai baiwa majiyar mu tabbacin bayanan duk da cewar ba a ba shi damar bayyanawa manema labarai ba, ya kara da cewar, ” akwai maganar mutanen da ke shigowa jam’iyya kuma su tsallake gobe zuwa wata jam’iyyar gobe”.
” Muna son daukar mataki akan masu shigowa jam’iyya dan kawai su na bukatar takara. Wannan na daga cikin tsarin da muke son gabatarwa dan samar da damar yin biyayya ga jam’iyya.
Anfani da tsarin baiwa ‘ya’yan jam’iyya takara ba bisa ka’ida ba ya saba. Domin ba wai shugaban jam’iyya zai tashi kawai ya bada tikitin takara ba, akwai bukatar bin ka’ida tare da bin tsarin yadda ya dace.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bin tsari wajen kashe kudaden jam’iyya yana daga cikin abinda za a yi gyara akai, domin dole a rika buga rahoton yadda aka kashe kudaden jam’iyya a kowani karshen shekara.
Majiyar tace sashe na 13 da 20 na kundin tsarin jam’iyyar na shekarar 2014 da aka yi gyara akwai bukatar mutunta shi. Sashen wanda kwamitin gyaran fuska ga tsarin dokokin jam’iyyar da tawagar Muiz Banire ta jagoranta karkashin shugabancin tsohon shugaban jam’iyyar, Cif John Odigie-Oyegun na kwamitin tsare tsaren jam’iyyar ta kasa ta jagoranta ya samu yabo.
Haka kuma, wakilan matasa a kwamitin riko na shirya tsare tsaren zaben shugabannin jam’iyyar, Ismaeel Ahmed, ya bayyana cewar tsarin zai baiwa matasa damar cin gashin kan su.
Ismaeel yace sabon tsarin da ake son gabatarwar, zai tilastawa zababbun shugabanni da wadanda ake nadawa da su koma mazabun su dan wayar da kan al’umma tsare tsaren jam’iyyar.
Shugaban matasan yace abu ne mai wahala ga shugabannin mu su iya komawa mazabunsu dan su hadu da ‘ya’yan jam’iyya a kallan a kowane watanni shida.
Abinda zai baka mamakin yadda ɗan jam’iyya zai zaku yana jiran zuwan shugaban kasa, ko shugaban majalisar dattijai, ko gwamna ko minista dan taron jam’iyya a matakin mazaba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

” Wannan zai taimaka hada kan jama’a da kyautata zaton su ga jam’iyya ta hanyar cigaba da samun kyakkyawan fahimta tsakanin shugabannin jam’iyya a matakin mazaba da shugabannin da ke wakiltarsu.
Zai taimaka wajen wayar da kan yayan jam’iyya na kasa dan sanin tsare tsare da shirye shiryen gwamnati,na zanta da shugaban kasa kuma ya yaba da tsarin. Ina tunanin ya kamata mu tabbatar da shi dokokin jam’iyya.
Muna shirin samar da canje canje ga jam’iyyar APC, dokoki da tsare tsaren zaben shugabanni na fitar da gwani, wanda mun tabbatar matasa za su samu damar taka rawa a ayyukan jam’iyya da tsare tsarenta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Muna duba yiwuwar gabatar da ajanda a jam’iyya ta yadda matasa za su samu damar taka rawar gani ta yadda zasu anfani duk wani kudurin cigaba siyasa a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *