Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya amince da sanya hannu a kasafin kudin badi, kasafin kudin da gwamnatin jiha ta mikawa majalisar dokokin jiha dan tantancewa.
Kasafin kudin wanda gwamnan ya sanyawa hannu a gidan gwamnati da shugaban majalisar, Rt. Hon Abdullahi Bawa Wuse ya samu wakilcin mataimakinsa, Hon. Jibrin Ndagi Baba mai wakiltar karamar hukumar Lavun da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar suka halarta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A lokacin da yake sanya hannu a kasafin da majalisar ta gabatar mai, gwamna Sani Bello yace kasafin kudin 2021 kasafi ne da aka takaita duba da yadda annobar COVID-19 ta mayar da jihar baya, kasafin ya mayar da hankali ne akan yadda tattalin arzikin kasa ke tafiya.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ya kara da cewar tattalin arziki yayi kasa saboda wannan matsalar, gwamnati ba za dunkule hannayenta ba, za ta yi anfani da dokoki wajen daga darajar hanyoyin samun kudin shigarta.
Gwamnan ya janyo hankalin al’ummar jihar da su kara hakuri da kuma baiwa gwamnati kwarin guiwa ta hanyar amincewa da harajin da aka dora masu ta hanyar biya ba tare da mayar da hannun agogo baya ba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yace kasafin kudin badi an takaita shi ne ta yadda za a samu damar kammala ayyukan da aka sanya a gaba, dan haka jama’a su fahimci yadda gwamnati ke da kudurin ciyar da jihar gaba.
Gwamnan ya yabawa yan majalisar dokokin jiha, wajen aiki ba dare, ba rana dan gaggauta gabatar da kasafin cikin lokaci, ya ba da tabbacin gwamnatinsa za ta gabatar da kasafin kamar yadda aka tsara shi.
Yace yan majalisar sun cancanci yabo ta yadda suka amince da kasafin ba tare da jinkiri ba ta yadda za a samu damar aiwatar da shi kan kari kamar yadda aka tsara.
Shugaban majalisar yace ainihin kasafin kudin ya wuce naira biliyan 151.2 kamar yadda aka gabatar masu, an kara shi da sama da naira biliyan 2.1.
Ya bada tabbacin cewar majalisar za ta sanya idanu dan ganin an aiwatar da kasafin kudin kamar yadda aka tsara.
Yace majalisar za ta cigaba da hada kai da sauran bangarora dan samar da dandanon mulkin dimukuradiyya ga jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *