Spread the love

A yau ne lahadi ake gudanar da za6en sabbin shuwagabannin da za su chigaba da jagorantar qungiyar ɗalibai ‘yan asalin Sokoto ta Arewa, Waton Associations Of Sokoto North indigen Students (ASONIS) bayan cimma wa’adin Shugabancin wayanda ke jagorantar kungiyar.

Kamar yanda aka saba yanzu haka zaben ya na kan gudana adakin taro na Aliyu Gare Hall, dakechikin Sokoto ta Arewa.

Matasa da dama musamman ɗalibbai wayanda ke da register da wannnan qungiyar sun yi chinkoso domin zaben yan takara da suke son su jagorance su a wannan karon.

Kamar yanda wakilinmu na managarciya ya tattauna da wasu mahalarta zaben sun nuna farin ciki da goyon baya Dan ganin yanda hukumar da ke da alhakin zaben sukayi tsari mai kyau a wannan karon.

Akwai jami’an tsaro da da manyan yan siyasa da mukarabayyen gwannanti a awurin musamman yan asalin karamar hukumar domin nuna son cigaban daliban yankinsu.

Babban makasudin assasa wannan kungiyar shine domin samun jagorori masu wakiltar daliban wannan karamar hukumar tare da gabatar da hidima ta musamman domin cigaban ɗalibban.

Shafiu Garba Reporter.
Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *