Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

Ranar lahadin makon da ya gabata ne mahara dauke da makamai suka aukawa garin Madaka dake karamar hukumar Rafi a masarautar Kagara, inda suka kashe mutane tare da yin awon gaba da hakimin garin Alhaji Zakari Ya’u Idris.
Bayan lokacin da aka dauka ana bincike koda za a gano mabuyan maharan, wanda kusan tun a safiyar littinin aka fantsama amma ba a samu nasarar hakan ba.
Rahotannin da ke fitowa yammacin asabar din makon nan maharan sun kashe hakimin kimanin kwanaki uku da suka gabata.
Masarautar Kagara da ke karamar hukumar Rafi na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fuskantar matsalolin mahara a jihar Neja, sauran sun hada da karamar hukumar Munya, Shiroro da Mariga, da Mashegu da Kontagora.
Zuwa yanzu dai bayan marigayi Alhaji Zakari Ya’u Idris maharan na rike da da hakimin Gunna da zuwa yanzu ba a san halin da yake ciki ba duk a masarautar ta Kagara bayan jama’a da dama da ke komar maharan, ban da wadanda suka samu nasarar kubuta daga yankuna da dama.
Masarautar ta shirya addu’ar rasuwar hakimin Alhaji Zakari Ya’u Idris a gobe lahadi.
Masu tada kayar bai suna cin karensu ba babbaka a arewacin Nijeriya, yakamata mahukunta su dauki mataki kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *