Muhammad M. Nasir.

Shugabannin jam’iyar APC a Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Alhaji Isa Sadiƙ Achida sun aminta da kakakin majalisar dokokin jiha Honarabul Aminu Muhammad Achida a matsayin halastaccen ɗan jam’iyarsu da ba su da kowace matsala da shi.
A hirar da Managarciya ta yi da shugaban a waya kan wasu na zargin sun aminta da kakakin majalisar ne don gudun kar jam’iyarsu ta dare gida biyu ganin ya halarci taron ɗaya daga cikin ‘yan takarar gwamna a jam’iyar Honarabul Abdullahi Salame kuma ƙarara ya goyi bayan takararsa abin da wasu magoya bayan jam’iyar suka nuna shishshigi ne ya yi don su ba su aminta da shi a APC ba, ya ce ba su da matsala da kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sadik Achida ya ce “harkar siyasa ce abin da ya faru ya faru mun barwa Allah, ba mu faɗa da kakakin majalisa ba abokin faɗan mu ba ne” a cewarsa.
Ya kara da cewar sun san ƙaddara sun yarda da abin da Allah ya yi.
Kalmominsa sun nuna sun gafarta wa kakakin majalisa abin da ake ganin kamar ba za su yi ba yanda ya kwance masu zane a kasuwa ya goyi bayan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kan jagoransu Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, a lokacin zaɓen wanda zai jagoranci majalisa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A jiya ne Kakakin majalisar ya ziyarci shugaban jam’iyar don taya shi murnar ba shi ragamar jam’iyar a matsatin riƙon ƙwarya anan ne ya yi jawabin da ya ja hankali in da ya nuna Sanata Wamakko ne jagoran tafiyar duk wani ɗan APC a Sakkwato.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *