Spread the love

Jaruma Hadiza Aliyu Gabon ta yi wa dattijon nan da ya bayyana mata yana sonta kuma in bai aure ta ba zai shiga wani hali, goma ta arziki in da ta faranta ransa.
Managarciya na ganin wannan kyautar kuɗi dubu 200 da ta aika wa dattijon a matsayin wayo da nuna fin ƙarfi cikin hikima ya je ya nemi daidai da shi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani faifan bidiyo da yake yawo a kafofin sada zumunta ya nuna tsohon yana cewa Hajiya Hadiza abin da kika ƴimin na alheri Allah ya yi miki nagode sosai da kuɗi dubu 200.
Ya ce yana jiran a saka rana kamar yadda ta ambata in an sa rana za a sanar da shi ya yi addu’ar ganin wannan rana.
Duk wanda ya kalli hoton zai tabbatar da saƙon da Gabon ke son isarwa na halinta na taimako da yanda halin tsohon yake yana buƙatar a taimaka masa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Amma alamu ya nuna tsohon bai gane wayon da aka yi masa kan farincikin da yake ciki na ganin Gabon ta san da shi har ta aiko masa da kuɗi kan soyayyar da yake yi mata.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *