Spread the love

  DagaMuhammad Awwal Umar, Minna.
  A satin nan da yake karewa ne wani mummunar al’amari ya faru a garin Kagara na jihar Neja,inda uwargida ta kona amaryarta da ruwan zafi tafasasshe.
Lamarin daya kai ga kotun majistare dake Kagara ta ingiza keyarta zuwa gidan gyara hali a garin  Kontogora.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Uwargida Maryam Yunusa ta bayyana cewar lamarin ya faru ne bayan ta sanya takalmin mijinta dan yin aikin cikin gida inda amaryar Hindatu ta tsegunta wa maigidan na su Malam Nura cewar tasanya takalmin shi, cikin fushi ya fito daga dakin amaryar ya bukaci ta ciretakalmin, wanda nan take ta cire.
A cewar Maryam, ‘bayan na cire takalmin na cigaba da hidimar da ke gabana, na taho zan wuce ita Hindatu na tsaye a bakin murhu da kofin ruwan zafi a hannunta, sai na buge ma ta hannun ban sani ba, nan take sai na ji ta fantsama min ruwan zafin a baya da kai ga na kone a gefen kuibi na.
‘Gaskiya kunar da ta yi sakamakon zubama ta tafasasshen ruwan zafin da na yi nata yafi na wa muni.
‘Ina bata hakuri da ta yafe min, in Allah ya yarda za mu yi zaman lafiya da ita hakan ba zai sake faruwa ba, domin na yi nadama matuka da na san abin zai zama haka daban aikata ba domin zafin zuciya ce ta sanya ni wannan abin.
‘Mun haihu da shi(mijinta),muna da yara tun shigowar Hindatu a gidan nan ba ma zaman lafiya saboda irin abubuwan da maigidan mu ke min, bai yin adalci a tsakaninmu a zaman takewar aure wannan abin yana bata min rai sosai. Injita.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ta ci gaba da cewa duk abindaya janyo wannan abin, na sanya ruwa a wutan lantarki, sai na kira shi yazo ya cire min, bayan ya zo ya cire sai ya bari a kofar dakina, ni kuma na zo zan yi daka na duba ban ga takalmi na ba sai na ari na shi na sanya, yadda ya fito dakinta a fusace ya umurci in cire mai takalmi ya bata min rai dan ina zargin ita ta tunzuro shi yayi min hakan, yayuna sun zo a lokacin sai ya kai karana wajen su, suka ba shi hakuri kuma su kai min fada, to bayan tafiyarsu ne wannan iftila’in ya auku.
Amarya Hindatu Hamisu ta ce da safe maigidansu bai fita ba, dan ya yi bacci yana tashi ya shiga wanka, ganin yadda takalmin sa su kai yi datti sai na goge masa, yana fitowa daga ban daki ya ga na goge takalmin, ya kira ni ya sanya min albarka, jin hakan sai ita Maryam ta kwashe takalmin ta sanya a kafarta ta ci gaba da aiki yana fito wa bai ga takalmi ba, sai na gansu a kafarta, sai na ke gaya masa cewar Maryamta sanya takalmin da na goge yanzun nan, idan ni na yi mata hakan ba za ta jidadi ba, yana fitowa ya umurci ta cire takalman, shi ke nan ta fara zagin shi,daga shi har iyayen shi, daman tun farko tace sai tayi ajalina, sai dai hakan yasa ta gidan aurenta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

“Ni ke da girki a ranar, kuma ga yan uwanta su biyu sun zo, yace a dafa taliya tunda ga baki sun zo amma bai da cikakken kudi a hannun shi, na dauko dari uku na ba shi nace ya kara a sawo taliyar.
“Bayan na kammala girki na zubawa bakin da ‘ya’yanta da ita kanta Maryam din, yace min tuwo za a yi da dare, ganinna kammala girkin rana sai na mayar da ruwan tuwo tunda ban kashe wutar da ke ci a murhu ba.Na taho ingyara wutar sai ta hankada min labulen daki ta ke ce masa ba ka ji ina kiran kaba ne, martanin da ya mayar mata, shi ne na ji ki je gani nan zuwa, tunda ta fara aikowa tana kiransa na ce yayi hakuri ya tafi ya ji kiran dan kar a sakesamun matsala.
“Bukitin dana debo ruwa a rijiya yana kusa da murhun da na ke girki, yana waje yana yimata magana, sai ta sauke ruwan tuwon ta zuba a bukitin kamar za ta yi wani abu daruwan, ina cikin daki a lokacin sai ta buɗe dakin kawai ta watsa min tafasasshen ruwan tuwon nan, shi ya mayar dani hakan da ka ke gani yanzu.
Ban haihu da shi ba, watan mu takwas da aure ke nan, ita dai ce ke da ‘ya’ya da shi, tun shigowa ta gidan nan ba mu zaman lafiya da ita, ni kan same ta in ce ma ta dan Allah tayi hakuri mu zauna lafiya, tunda Allah ya kaddare mu da zama da miji daya.” a cewata.
Ta ce Maganar baya mata adalci ba gaskiya ba ne, duk lokacin da ta bukaci abu sai yayi mata,har omon wanki a kullun sai ya saya mata, idan na bukata sai yace min bai da kudi, amma ina dannewa saboda zaman aure na taho yi, ina da ɗan halin da ni ke yiwa kaina har in taimaka masa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

‘Kamar yadda tace min sai ta halaka ni, yau na ga zahiri gaskiya, domin ta gama da rayuwata, ni kadai na san yadda ni ke ji a jikina.Kishi ba abu ne mai anfani ba, ya kamata su ajiye kishi waje daya su rungumi kaddarar Allah,kowace rayuwa da kaddararta, idan Allah yasa sai mijin ki ya auri mata da yawa ki zama mai hakuri sai ki zauna lafiya a rayuwar ki.’
Zuwa yanzu kotun majistare mai mazauni a Kagara ta ingiza keyar Maryam Yunusa gidan gyara hali na Kontagora.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *