Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya mika gaisuwar ta’aziyar rasuwar mahaifin Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso gare shi da danginsa gaba daya.
A wani bayani da daya daga cikin mataimakansa kan yada labarai Ibrahim Bashir ya fitar ya ce Wamakko ya yi ta’aziyar rasuwar Alhaji Musa Sale Majidadin Kano Makaman Karaye ga iyalansa wanda ya rasu da sanyin safiyar yau Jumu’a yana da shekarru 93 a duniya.
Ya roki Allah ya gafarta masa ya baiwa danginsa hankurin rashinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *