Spread the love

Tabbas an san tarbiya daban shiriya daban!

Amma ya kamata uwaye su san cewa,ba fa suka dai ne ke da hakki akan ‘ya’yansu,su ma ‘ya’yan nada cikakken haki akan su,duba da yadda annabi yace acikin hadisi cewa “KULLUKUM RA’IN, WA KULLUKUM MAS’ULUN AN RA’IYATAHI”
Ma’ana dukan ku makiyaya ne,kuma za’a tambayeku akan kiyon da aka baku.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kuma acikin alqur’ani Allah ya na cewa “Ku anfusakum wa halikum naran,wa kudu hannasu wal hijaratu alaiha mala’ikatun gilazun shidadun.” Har zuwa karshen ayar,
Wadda ita wannan ayar kai tsaye tana nuna cewa ba fa kai kadai zaka tseratar da kanka daga wuta har da iyalinka.

Mata masu kananun shekaru,sun fantsama cikin rayuwar kunci akan iyayen su,
Jarabta za ta iya saukowa kowa,ba wani mutum da yafi karfin Allah ya jarabce shi da kowa ce irin kaddara. Kuma duk yadda iyaye na kai ga tarbiya bazai hana wannan kaddarar ta fada kan ‘ya’yan su ba,madamar Allah ya so da hakan.

Akwai mata da yawa wadanda na zama rikakkin karuwai wadanda iyayensu sune suka fi kowa laifi acikin wannnan tafiyar
Yarinya takan hadu da jarabtar cikin banza, maimakon ace iyaye su jata a jiki,su nuna mata muni da aibun wannan danyen aiki,da kuma illar sa ga addini da kuma al’adu, a’a ba haka za su yi ba,kokarin korarta za su yi ga duniya,tare da sabon katin yarjewa akan wannan hanya,su na son ta je gaba ta kara gogewa,ta zama cikakkiyar ‘yar iska.

Wai wannan shi ne tsololuwar horon da za su aikata gare ta,wanda sam ba wata tsoratarwa da yarinyar za ta ji,kuma zuciyarta zata kekashe,idanunta za su bushe,tsana zata karu acikin zuciyarta ta mutane,kullum tunanin ta,bata da sauran zama wata ‘ya mai cikakken ‘yanci,ko kuma zata dauki kanta wata halitta marar mamora cikin al’ummarta.

Minene alfanun korar musamman ga diya mace,akan wani laifi da ta aikata,wanda kuma bata da wata hanyar da zata bi don ta goge kaddarar dake bayanta, tunda bata san kebantaccen ilimi na gaibu ba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Hakan me ya ke nufi?
Fushi da ubangiji ko me?
Shin ubangiji bai isa yayi duk abinda ya ga dama ga bayinSa ba?

Ku iyaye don kun kori ‘ya’yanku shi zai sa ku huce takaicin da kuke shaka sanadiyar wannan?
Ni dai ina ganin wannna magana bata nufin komai,sai son nunawa Allah mi na yi masa ya jarabce ni da wannan fitinar. Ko kuma fito-na fito ga ubangiji, tare da zanga-zangar dole sai ya cire mummunan kaddara acikin ahalinmu.
Iyaye ba ku isa ku sauyawa Allah duk wani tsari akan bayinsa ba,don haka mafita daya ce,idan har an jarabce iyalinmu ta kowane fuska,kora da wasu maganganu da muke musu,masu kama da tsinuwa,ko kuma kiran Allah ya halakar da wance, addu’a tafi komai muhimmanci ga rayuwarmu,kuma an san albarkar iyaye ta shallake duk wata addu’a.
Ya kamata wadannan yaran ajawo su ajiki a nuna musu kauna da soyayya tare da munin wannan rayuwar da suka jefa kawunan su aciki.
Ba’a kori mace ba,korar bata haifar da komai sai karin tabarbarewa tarbiya.

Yakamata iyaye su fahimci su masu bayar da tarbiya ne ba masu shiryarwa ba, abin da yakamata su yi bai wuce yin abin da Allah ya daura masu in ya jarabe su aikin da suka yi kar su yi kasa a guiwa domin shiriya tasa ce yana ba da ta ga wanda ya ga dama.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Duk mahaifin da ya kasa tarbiyar dansa Allah zai tambaye sa, don haka a yi kokari a kawo a fahimci nayin da Allah ya daura kan mahaifa.

Dafatar iyaye za su fahimci wannan.

Allah ya sa mu dace,Allah ya bamu ikon cin dukkan wata jarabta.
Nagode
Zainab Aliyu Sifawa

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *