Matsalar tsaro: Karamar hukuma a Sakkwato ta dauki ‘yan sa-kai don kare rayukka da dukiyoyin al’ummarta

Daga Shafiu Garba Reporter Sokoto.

Karamar hukumar Binji dake jihar Sokoto ta dauki ‘yan sa- kai da ake kira ‘yan banga a jihar domin taimakawa sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da kare rayukka da dukiyoyin al’umma a yankin daga barazanar ‘yan fashi da masu satar mutane da mahara.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaban karamar hukumar na riko Alhaji Wadata Muhammad MaiKulki, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai kan matsalar tsaro a yankin.
MaiKulki ya ce matakan da aka dauka domin kare lafiyar karamar hukumar, majalisar karamar hukuma ta gyara daya daga cikin motocin aikin ‘yan sanda a yankin.
“Mun kafa kungiyar jami’an tsaro da ke zagayawa kauyukanmu da garuruwanmu don tabbatar da ‘yan fashi da sauran masu aikata laifi ba su samun sararin numfashi ba.

“Kuma wannan matakin yana da amfani, saboda duk masu ba su bayanan dake yankin an kama su kuma ‘yan sanda sun gurfanar da su” inji shi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Babban jami’in gudanarwa, wanda shi ma yake gudanar da mafi yawan ayyukan, ya lura cewa an baiwa majalisar kwarin gwiwa, musamman ga ‘yan banga.
Ya yaba wa sojoji da sauran jami’an tsaro a yankin kan yadda suka amsa kiran gaggawa.
Mai Kulki, wanda ya jaddada mahimmancin ilimi wajen magance ta’addancin ‘yan ta’addan, ya ce; “Wasu mutane sun shiga kungiyar ‘yan fashi ne saboda ba su san abin da ya shafi addini ba.
“Wasu daga cikinsu ba su da ilimin addinin Musulunci na asali, saboda haka ba su san ma’anar addini na kashe rai ba tare da kowane laifi ba.
“Saboda wannan ne muka gyara makarantun Islamiyya dana karatun yamma da yawa a kauyukanmu muka shiga yekuwar wayar da kan jama’a game da mahimmancin ilimi ga rayuwarmu,” in ji shi.
A cewarsa, majalisar ta kuma gyara dakin shan magani da Masallatai da sauram abubuwan more rayuwa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *