Spread the love

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi ta’aziya ga tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso kan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Makaman Karaye.
Gwamna ya bayyana rasuwar wadda ta girgiza shi ta sa shi bakinciki a lokacin da ya samu labari “Mun tabbatar da uba nagari ya tafi” a cewarsa.
Gwamnan ya ce lalle jin zafin rashinsa ba zai taba gushewa a tsakaninmu ba, ya zamar musu jagora da ya ke koya masu hakuri da kyawawan dabi’u da za a koyi da mai masu a rayuwa.
Gwamna ya ce lalle Kano ta yi rashin daya daga cikin diyanta, amadadin gwamnati da mutanen Kano ina mika ta’aziyar rasuwar mu ga tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da dangi da masarautar Karaye kan rashin Makama Baba Musa Sale Kwankwanso da ya rasu yana da shekara 93 a duniya.
Allah jikansa da rahama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *