Spread the love

Daga Shafi’u Garba Reporter Sokoto.

A kalla likita 20 ne suka rasa rayukkansu sanadin cutar Korona dake addabar Nijeriya da duniya, kungiyar likitoci ta kasa reshen Abuja ce ta sanar da hakan.
Shugaban na reshen Dakta Enema Amodu ne ya sanar da hakan a Alhamis da ta gabata a zantawarsa da wasu manema labarai.
Ya ce a sati daya kawai sun rasa kwararrun likitoci manya da kanana da wasu gingima-ginman likitoci sanadin covid 19.
“Hakan ya nuna kwayar cutar tana tare da mu kenan.” A cewarsa
Ya ce duk da hadarin da likitoci ke sa kansu alawus na su a wata 5000 ne kawai.
Ya yi kira Kakakin majalisar wakillan Nijeriya Femi ya yi hobbasa a duba tsarin biyan alawus din domin da yawan likitocin suna wahala wasu na mutuwa.
Ya yi fatar gwamnati ta duba tsarin biyan alawus din a sabuwar shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *