Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

Tsohon Grand Kadi kuma Malamin addinin musulunci a jihar Neja, Sheikh Ahmed Lemu ya kwanta dama.
Shehin malamin ya rasu safiyar yau alhamis 24 ga watan Disamba a Minna, yana shekaru 91 da haihuwa.
Sheikh Lemu ya rubuta littattafan addinin musulunci da dama da duniyar musulmi ke anfani da su yanzu.
Shehin malamin ya taba samun lambar yabi ta Sarkin Faisal Abdulazeez akan gudunmawar da yake baiwa al’umma a bangaren karantarwa da taimakon jama’a a shekarar 2014, da iya mu’amala da wadanda ba musulmi ba.
A wata takardar da ta fito daga iyalan mamacin, wadda Sheikh Nuruddeen Ahmed Lemu ya sanyawa hannu ya bayyana cewar yanzu haka shirye shirye sun nisa wanda da an kammala za a rufe mamacin yau, inda za a gudanar da sallah misalin 12 na safiyar yau a babban masallacin juma’ar cikin garin Minna.
Allah yawa Sheikh Ahmad lemo, Rasuwa, kamin rasuwarsa, shi ne shugaban IET na farko, nan jihar Sakkwato lokacin gwamnan soja margayi Usman Faruq, kamin ya koma Minna, jihar Niger da aiki, yayi littattafai da dama, na addinin Musulunci da shi da Mai dakinsa Aisha lemo, Allah shi gafarta masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *