Aƙalla mutane 16 sun rasu a garin Jaba cikin ƙararamar hukumar Moro a jihar Kwara lokacin da motar dakon mai waton tanka take ɗauke da mai ta ƙwacewa direba a unguwar Gaika, sama da gidaje 30 da dukiyoyi ne suka kama da wuta.
Manema labarai sun samu bayanin lamarin ya faru wuraren ƙarfe 9 na safen ranar Laraba sanda direban motar ke tuƙi a saman hanyar Gaika a cikin Jaba motar ta ƙwace masa.
Motar ta tabi wata ne ta kusa da ita ta bugi gina sai wutar ta kama gaba ɗaya anan ne fetur ya riƙa zurara yana ƙara wa wutar tashi.
Gwamnan jijar Kwara Abdulrahman Abudulrazak a bayanin da ya fitar ya jajantawa iyalan mamatan da waɗanda suka yi hasarar dukiyoyinsu ya ce abu ne na ɓacin rai da baƙinciki.
Ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta yi hanzarin gano yawan dukiyar da aka yi hasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *