Spread the love

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya rantsar da zababbun shugabannin kananan hukumomin Borno 27 cikinsu akwai farfesa guda biyu da Dakta a jami’ar Maiduguri guda don farfadowa da kananan hukumomi.

Farfesa Adamu Alooma, an rantsar da shi shugaban karamar hukumar Damboa sai Farfesa Ibrahim Bukar a Gwoza. Dukansu an zabe su ne a zaben da aka gudanar a 28 ga watan Nuwamba in da APC ta lashe zaben gaba daya.

Haka ma akwai mai digiri ta uku Dakta Ali Lawan Yaumi, da zai shugabanci Magumeri.

A wurin rantsuwar Zulum ya tuna a yau shekara 10 an kasa gudanar da zaɓen domin matsalar tsaro a jihar

Gwamna Zulum ya umarci ma’aikatar kananan hukumomi da sauri ta mikawa sabbin zababbun shugabanni dukan kudadensu da ake ba su daga asusun gwamnatin tarayya ba tare da sun rage ko naira ba domin samun sauyi ga rayuwar talakawa.

Gwamnan ya roki shugabannin su yi aiki da tsoron Allah ba tare da yin wata alfarma ko tsoron wasu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *