An yi kira ga gwamnan Neja da ya saisaita rikicin APC a jihar kafin ya fita waje

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.

An nemi gwamnan Neja Alhaji Abubakar Sani Bello da ya tabbatar yayi amfani da wannan damar wajen dunke barakar rashin fahimtar da ta taso a jihar Neja. Kodinetan goyon bayan takarar Tinubu, Injiniya Kabiru Abdulhamid Tafa ne yayi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yace yanzu haka uwar jam’iyya ta kasa ta riko bisa jagorancin gwamna Mai-Mala Buni ta umurci kwamitin sulhu da ya tabbatar da walwale matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta a sassan jahohi, wanda ya baiwa sanatoci da wasu ‘yan majalisar wasu jam’iyyu dawo wa jam’iyyar APC.
Yana da kyau kamar yadda maigirma gwamna yake kokari a wasu jahohin ya tabbatar ya dunke barakar da ke cikin gidansa, domin bai kyautu kana aiki a waje ba alhalin gidan ka na cikin wani hali.
Tsakanin maigirma gwamna da tsohon shugaban jam’iyya matsalarsu ba matsala ce da ba za a iya warwarewa ba, ko ma ke faruwa idan aka yi hakuri zai wuce, amma idan aka cigaba da tafiya haka gaskiya abin ba zai haifarwa APC da mai ido ba, ina kira ga dukkan bangarorin nan da su kai zuciya nesa su zauna akan teburin sulhu tafiya kai a rarrabe bai haifar da komai sai koma baya.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Maganar sabunta rajistan jam’iyya ga yayanta abu ne mai kyau, domin shugaban riko na kasa yana da tabbacin hakan zai baiwa jam’iyyar damar samun masu sha’awar shigowa da za su taimaka wajen bunkasa jam’iyyar, kowa yasan irin gyaran da aka yiwa jam’iyyar nan ko yau ka shigo daidai ka ke da wanda aka kafa jam’iyyar da ita kuma yana da damar yin takarar kowani irin matsayi ba kamar wasu jam’iyyun da ke cewa sai ka kai adadin wasu shekaru ba. Duk lokacin da mutum ya shigo jam’iyyar APC muna marhabin da shi.
Wannan kuduri kokari ne na bunkasa jam’iyyar, domin duk lokacin da ka bar kofar ka a bude a tafiyar siyasa za ka ga cigaban da baka taba gani ba, saboda siyasa ana yin ta ne dan jama’a kuma jama’ar nan ake bukata. Wannan hanya ce mai bullewa, domin zuwan Mai-Mala ya taka rawar gani sosai, domin an samu gwamnan da ya bar jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC, an samu karin sanatoci da yan majalisun tarayya da suka dawo APC ka ga ai cigaba ne mai anfani, duk abinda ka ga an kawo a wannan tafiyar to cigaba ne mai anfani.
Yana da kyau shugabannin mu a jihar Neja su tsaya su dubi wannan matsalar cikin gida da muke fuskanta, wadanda ma ke da korafi a kotu da a shawarce su da su janye, a zauna ayi magana ta dattako domin a samar da alkibla mai dorewa. Da bangaren tsohon shugaban jam’iyyar, Injiniya Jibrin Imam Gawu, da bangaren shugaban riko Sa’idu Galko duk yayan jam’iyya ne, muna da dattijai, ya kamata gwamna ya hada kawunan su dan yiwa jam’iyya aikin da ya dace.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Maganar riko ai watanni biyar ne kacal, ban ga abin tada jijiyar wuya ba a nan muna fuskantar zaben shugabannin jam’iyya idan muka tafi kai a rarrabe, lallai ba zai haifar mana da da mai ido ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *