Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Gwamnatin Jihar Sokoto karkashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta raba kudade ga kiristoci mazauna Sokoto domin su kara a shagulgulan bikin kirsimeti.

Shugaban jam’iyyar PDP na jiha Honarabul Bello Aliyu Goronyo ne ya jagoranci raba kudaden a madadin gwamnati.

An raba kudaden a ofishin jam’iyar ga kungiyoyin kiristocin don a karrama su da a nuna masu gwamnatin jiha na tare da su.
Wannan tallafin shi ne irinsa na farko da aka ga jam’iyar ta raba da har ya jawo hankalin mutane abin da ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin magoya bayan jam’iyun PDP da APC a Sakkwato.
Masu sharhi kan lamurran yau da kullum sun kalli wannan tallafin a matsayin siyasar 2023 ganin yanda ake hasashen Tambuwal zai nemi tsayawa takarar shugaban kasa.
Managarciya ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na PDP Honarabul Abdullahi Yusuf Hausawa don sanin yawan mutane da kungiyoyin da suka amfana da kuma yawan kudaden da aka ba su.
Hausawa ya ki aminta ya karba tambayoyin da wakilinmu ya yi masa.
Mutane sun yi hasashen kudi ne masu yawa aka ba su ganin yanda kungiyoyin suka bar wurin cike da murna da mamakin karamcin da aka yi masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *