Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Sabon zababben shugaban majalisar matasa(NYC) ta kasa reshen jihar Sakkwato Ambasada Yakubu Abubakar ya yi alkawalin zai yi tafiya tare da wadanda suka nemi kujerar a tare domin dukansu abokai ne masu son ciyar da Sakkwato a gaba.

Yakubu jim kadan bayan kammala kirga kuri’a wadda ta nuna shi ne ya lashe zabe in da ya samu  kuri’ar 241 abokin takararsa  Yusuf Muhammad ya samu  62, daga cikin kuri’un da aka jefa, yace ya yi murna sosai ya godewa Allah, wadanda suka gudanar da zaben sun yi adalci matuka.

Ya kuma nuna farincikinsa yanda abokin karawarsa ya taya shi murnar lashe zaben.

Shugaban kwamitin rikon kwarya da gudanar da zabe Abubakar Dangaskiya ya ce ya yi farinciki da kammala wannan aiki cikin nasara da cika alkawalin da suka dauka na gudanar da zaben majalisar matasa sahihi kuma ingantacce, ‘Muna godiya ga dukkan wadan da suka ba da gudunmuwarsu a zaben musamman mutum 36 da aka daurawa nauyin gudanar da aikin, wannan ya sa Sakkwato za ta zama abar koyi a Nijeriya’ a cewar Dangaskiya.   

Kwamishinan ma’aikatar matasa Bashir Gorau a kalamansa lokacin da yake bayar da damar a fara zabe ya ce  Wadanda aka tantance ne suke zaune anan, ‘Ba za mu bari wani ya hargitsa mana wuri ba, ba nuna bambancin siyasa, kar ku bari a yi siyasa anan, duk wanda  ya jefa kuri’a sai an kirgata, cigaban matasan Sakkwato muke magana don haka ba ruwanmu da bambancin jam’iyar siyasa’. A cewar Kwamishina.  

Wannan zaben na shekarar 2020 ya zama zakaran gwajin dafi domin matasa ba su taba ganin an bas u damar zaben shugabanni ba sai yanzu.

An dauko mutane 113  kungiyoyin sa-kai 66, kowace mutum uku  da wasu a  kananan hukumomi  23 kowace biyar yawansu zai  kai 198 su ne suka zabi sabbin shhugabannin majalisar guda 17.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *