Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya dawo kan aikinsa na gwamna bayan da sakamakongwajin da aka yi masa ya tabbatar baya dauke da cutar Korona.

Gwamna Tambuwal ya sanar da haka a wata takarda da ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai ya ce “Bana dauke da cutar covid 19 a lokacin da na killace kaina an yimin gwaje-gwaje da bin sharuddan kariya daga cutar.

“Ina godiyar Allah da sanar da al’umma musamman mutanen Sakkwato sakamakon gwajin da aka yimin ya bayyana cewa ban dauke da kwayar cutar covid 19.” A cewar Tambuwal

Ya godewa mataimakinsa Muhammad Manir Dan’iya da ya kula da tafiyar da gwamnati a lokacin da yake killace.

Ya yi kira ga mutane su rika biyayya ga sharuddan da aka gindaya masu domin kariya da cutar ta Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *