Spread the love

PDP sun ziyarci kwamishinan ‘yan sanda na Sakkwato don ƙarfafa dangantakar aiki

Daga Muhammad M. Nasir.


Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sakkwato Alhaji Ibrahin Ka’oje ya karbi shugabannin jami’iyar PDP a Sakkwato ƙarƙashin jagorancin shugaba na jiha Alhaji Muhammad Bello Goronyo.

A jawabin shugaban ya ce manufar kawo ziyarar don karfafa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da jam’iyar PDP domin su yaba da yadda hukumar ke yi a wurin yaƙar ‘yan ta’adda, za su ba da gudunmuwa a yunkirin tsaftace jiha daga aiyukkan ɓata gari.


CP Ibrahim Ka’oje ya yi farinciki da ziyarar ya roki jam’iyar mai mulki a jiha ta kara ba su giyon baya ga kara samar da tsaro da kawo cigaba a jiha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *