Spread the love

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna.


Gwamnan Neja kuma shugaban gwamnonin arewa ta tsakiya, Abubakar Sani Bello yace lokaci da jahohin arewa ta tsakiya za su fuskanci matsalolin da ke damun yankin ya zo.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a dakin taro na banquet a lokacin karrama yankin arewa ta tsakiya a garin Makurdi ta jihar Binuwai.

Yace idan ana son yankin ya samu cigaban da ake bukata ya kamata taron kungiyar ya rika yawo a cikin jahohin yankin.

Ya bayyana bukatarsa akan yadda yankin arewa ta tsakiya za ta iya samun canji a kankanin lokaci, gwamnan yace shirya taro irin wannan akan kari zai taimakawa kungiyar zai taimaka wajen fuskantar matsalolin da yankin ke ciki musamman matsalar tsaro, ayyukan raya kasa, tattalin arzikin kasa da siyasa da wasu batutuwa masu muhimmanci.

Gwamnan ya bayyana cewar wannan shekarar mai karewa a matsayin shekara mafi kunci da ‘yan Najeriya suka fuskanta, ya roki Allah ya karawa yan Najeriya kwarin guiwa da juriya.

Kungiyar ta bayyana cewar akwai bukatar kusanci da juna ta hanyar hada hannu wajen cigaban kasar nan.

Wanda ya dauki nauyin shirya taron karrama gwamnonin, gwamnan Binuwai, ya yabawa takwarorinsa gwamnonin yankin da suka yarda su zama tsintsiya daya wajen hadin kai da cigaban yankin.

Gwamna Samuel Ortom ya yabawa shugaban kungiyar gwamnonin na arewa ta tsakiya wajen shirya wannan taron a Makurdi ta jihar Binuwai, domin dukkan matsalolin kasar nan yana dabaibaye da siyasa, kabilanci da bambancin addini, yace matsalolin za su yi wahalar walwalewa ganin an kirkiro su da dadewa, akwai bukatar dawo da soyayya, hadin kai kamar yadda gwamnonin mu suke fatar gani dan walwale matsalolin cikin sauki.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da ya samu halartar taron, ya bayyana cewar jahohin arewa ta tsakiya su ne ginshikan da ke rike da arewa da kudancin kasar nan,  ya bukaci jahohin da su tashi tsaye gaba daya tare da ajiye bambance bambancen da ke tsakanin su na siyasa ko kuma su cigaba da fuskantar abinda ba su yi tsammani ba.

Ya bayyana cewar al’umma na da yawa, bunkasar yankin ta hanyar kasuwanci zai iya kawo cigaba mai anfanin yankin.

An gabatar da wasannin gargajiya dan nuna irin kyawawan al’adun mutanen Binuwai wanda ya shafi kabilun jihar na kyawawan al’adun su.

Wanda ya bada damar fitar gwamnonin da kayan al’adar mutanen Binuwai wanda gwamnan jihar ya jagoranta.

    

    

    

    

    

  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *