Spread the love

 
Daga Comr Abba Sani Pantami.


Kwamitin shugaban kasa da ke yaki da annobar corona, ya sake bayar da umarni ga ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa kasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.


A cewar kwamitin wanda ke karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, duka makarantu a faɗin ƙasar za su zama a rufe har zuwa watan Janairun 2021.


Kwamitin ya bayyana cewa gidajen rawa da wuraren shan barasa da kuma wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a Abuja babban birnin kasar.

Covid 19 ta shigo a Nijeriya a karo na biyu kuma anason daukar matakin da yakamata, domin kariya daga cutar ta Kurona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *